Bayan Watanni 3 a Rufe : Yau Litinin za’a koma Makarantu a Zamfara

21BE085C 5E56 4883 A990 A9EE8C6B4309
21BE085C 5E56 4883 A990 A9EE8C6B4309

A ranar Lahadi ne gwamnatin Zamfara ta sanar da bude wasu makarantun firamare da sakandare a ranar Litinin 17 ga watan Janairu.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Malam Shehu Ibrahim, mukaddashin Daraktan tabbatar da ingancin aiki a ma’aikatar ilimi ya fitar.

Sanarwar ta ce makarantun gwamnati da masu zaman kansu waɗanda ma’aikatar ta ware a matsayin “kore” da “rawaya” ya kamata su koma don ayyukan ilimi na yau da kullun.

“Duk da haka, makarantun da ke cikin “ja” zasu ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da yanayin tsaro ya inganta,” in ji Ibrahim a cikin sanarwar.

Makarantun dai na ci gaba da komawa ne biyo bayan rufe dukkan makarantun a ranar 1 ga Satumba, 2021, lokacin da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 80 da malamai uku daga makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kaya a karamar hukumar Maradun (LGA).

Daga baya biyar daga cikin daliban sun tsere kwanaki kadan bayan sace su yayin da sauran dalibai 75 da malamansu aka ceto daga baya.

A baya ‘yan bindigar sun yi garkuwa da dalibai mata 279 na Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Jangebe a karamar Hukumar Talata Marafa.

Duk da haka ‘yan bindigar sun sako dukkan ‘yan matan a ranar 2 ga Maris, 2021 bayan tattaunawa da gwamnati da dama.

“Jami’ai daga ma’aikatar ilimi da kuma daraktocin shiyya za su zagaya don ganin matakin da aka bi,” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here