Ba zan sake tsayawa takara ba a 2027, domin Lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagoranci – Ɗan majalisar tarayya

HOUSE OF REPS MEMBERS 720x430

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki, ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba a zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Dasuki ya ce wannan shawara tasa ta samo asali ne daga ƙudurinsa na ƙarfafa dimokuraɗiyya ta hanyar bai wa matasa damar shiga gwamnati.

Ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka sadaukarwa ce ta kansa domin buɗe hanya ga sabbin matasa su shiga cikin jagoranci a Najeriya.

Ya ce, wannan mataki ba saboda gajiya ko rashin gamsuwa ba ne, amma wani kiran alheri ne da ya samo asali daga imani da fata na ganin sabuwar Najeriya mai ci gaba.

Dasuki, wanda ya fara harkar siyasa tun a shekarar 2011, ya taɓa zama ɗan majalisar dokokin jihar Sokoto, sannan ya riƙe mukamai a majalisar zartarwa ta jihar kafin ya zama ɗan majalisar tarayya daga Kebbe/Tambuwal.

Har ila yau, shi ne wanda ya kafa ƙungiyar “Ci gaban mu ya ta’allaƙa kan ayyukan mu na yanzu” The Future Is Now Project, wadda ke fafutukar ganin kashi 70 cikin 100 na kujerun majalisar wakilai sun kasance a hannun matasa ‘yan ƙasa da shekara 40 kafin zaɓen 2027.

Ya ce duk da cewa shi ma matashi ne, amma ya zarce shekara 40 da ƙungiyar ta tsara, don haka ya yanke shawarar bai wa sabbin matasa dama su fito su jagoranci.

Yayin da yake tunawa da tafiyar siyasar sa ta shekara 14, Dasuki ya gode wa mazaɓarsa da kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, bisa goyon baya da amincewa da suka nuna masa tsawon lokaci.

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa ta hanyar ba da shawara, jagorancin matasa da ƙarfafa manufofin da ke inganta shugabanci.

Dasuki ya bayyana burinsa shi ne barin tarihi wanda zai zama abin koyi ga shugabanni da ke sanin lokacin da ya kamata su ba wa sababbin ƙarni dama wajen jagoranci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here