Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa yana shirin janye burinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa domin ya baiwa wani ɗan takara.
Rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya nuna shirinsa na janyewa domin bai wa wani matashi mai ƙarfi da karɓuwa damar tsayawa takara a inuwar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a yayin hira da gidan rediyon BBC Hausa a ranar Laraba.
Sai dai Atiku ya bayyana labarin a matsayin kuskuren fahimta daga hirar da aka yi da shi.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a ranar Alhamis, yace babu inda Atiku ya nuna ko da alamar cewa zai janye wa wani ɗan takara.
Labari mai alaƙa: A shirye nake na ja da baya idan matashi ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyyar ADC – Atiku
Sanarwar ta ce: “Bayan tantance bidiyo da rubutaccen sakon hirar da aka yi da shi a harshen Hausa da kuma fassarar Turanci, babu inda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya faɗi ko ya nuna cewa zai janye wa wani ɗan takara.
Abin da ya faɗa a sarari shi ne, matasa da sauran masu sha’awar tsayawa takara su na da damar shiga takarar, kuma idan ɗan takara matashi ya fito ta hanyar sahihin zaɓe a cikin jam’iyya, zai mara masa baya ba tare da wata jinkiri ba.”
Ya ƙara da cewa, yayin da fassara da nazari na aikin jarida suka zama ruwan dare, yin hakan har ya kai ga yaudarar jama’a abin da bai dace ba ne, kuma bai kamata a ƙarfafa irin wannan ba.
NAN













































