Ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da gawarwaki Sama da 500 a Neja

images 5 6
images 5 6

Al’ummar garin Mariga da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja na ci gaba da neman gawarwaki sama da 500 da ake zargin ambaliyar ruwa ta tafi da su.

Babban Limamin Masallacin Mariga, Alhaji Alhassan Na’ibi, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Kasa NAN ta wayar tarho ranar Talata.

Ya ce “Yanzu muna neman gawarwaki sama da 500 da aka binne a makabarta a garin Mariga wadanda muka yi imanin cewa ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su a Mariga.”

Nai’bi ya ce al’ummar yankin sun shiga rudani, domin sai da aka kwashe wasu gawarwaki kimanin 100 daga makabarta zuwa wata makabartar domin dakile faruwar lamarin.

Babban Limamin wanda ya alakanta matsalar da ayyukan masu hakar ma’adanai da ke kusa da makabartar, inda ya koka da cewa ba su taba fuskantar irin wannan yanayin ba a cikin shekaru 60 da suka wuce a makabartar.

Sai dai ya yi kira ga gwamnatin jihar Neja da ta gaggauta kawo musu dauki domin dakile lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here