Akwai yiwuwar Gwamantin Tarayya kwace kadarorin kamfanin Jirgin sama na Dana don mayar da kuɗin ga gasinjoji da dillalan shirya tafiye-tafiye

Dana Airlines new

Gwamantin tarayya ta bayyana yiwuwar kwace dukiyar Kamfanin Jirgin Sama na Dana domin a sayar da su, a biya fasinjoji da dillalan tafiye-tafiye da kuɗinsu ya makale tun bayan dakatar da aikin jiragen kamfanin.

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya ce matakin zai tabbatar da kare haƙƙin jama’a da suka yi asarar kuɗi.

A cewarsa, taron masu ruwa da tsaki na zangon ƙarshe da ma’aikatar ta gudanar a Abuja ya tanadi inganta tsarin ayyuka ta hanyar sauraron rahotanni da korafe-korafe na jama’a, domin warware matsalolin da ke barazana ga ci gaban harkar jiragen sama a ƙasar nan.

Ministan ya nuna cewa Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Ƙasa za ta gudanar da bincike kan dalilin da ya sa kuɗaɗen fasinjoji da kamfanin ya rike har yanzu ba a mayar da su ba, duk da cewa hukumar ta dakatar da kamfanin ne saboda rahotannin da suka nuna kin biyayya a fannin tsaro da bin ƙa’idojin aiki.

Ya ce rahotannin tsaro da aka samu sun bayyana kasancewar hatsari idan kamfanin ya ci gaba da gudanar da tashi, abin da ya sa aka fifita kare rayuka fiye da duk wani abin da ya shafi kasuwanci.

Ya bayyana cewa hakan ya tabbatar da wajabcin dakatar da Kamfanin Jirgin Sama na Dana.

Keyamo ya sanar da cewa an umarci hukumar da ta nemo cikakken hanyoyin da za a tabbatar da cewa fasinjoji da dillalan tafiye-tafiye sun samu kuɗaɗensu, musamman idan masu kamfanin ko wasu da ke da alaƙa da shi suna ƙoƙarin sake shiga harkar jiragen sama ta wata dabara ko sabon rajista.

Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Ƙasa za ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa duk ‘yan Najeriya da ke bin kamfanin kuɗi sun samu hakkokinsu ta hanyar dukiyar da za a karɓa bisa doka, tare da tabbatar da cewa irin wannan lamari ba zai sake faruwa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here