Kyaftin din tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa kuma ɗan wasan Najeriya da ya fi kowa yawan wakilci a matakin ƙasa Ahmed Musa ya sanar da yin ritaya daga tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, lamarin da ya kawo ƙarshen gagarumar tafiya ta tsawon shekara 15 yana sanye da koriyar riga da fari ta ƙasa.
Ahmed Musa ya bayyana wannan matsaya ne ta shafukansa na sada zumunta da aka tantance, inda ya waiwayi tafiyar da ta fara tun yana da shekara 17 lokacin da aka fara kiransa zuwa wakiltar ƙasa a karon farko.
A tsawon shekarun nan, Ahmed Musa ya zama ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasan ƙwallon ƙafa da suka fi tasiri da samun yabo a Najeriya, inda ya kafa tarihi da wasanni 111 da ya buga wa tawagar ƙasa, adadin da babu wanda ya kai shi a tarihin ƙasar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, a cikin doguwar tafiyar gudanar da aikinsa na kasa da kasa, Ahmed Musa ya lashe kofin Afirka tare da tawagar ƙasa, sannan ya rubuta sunansa a tarihi a matsayin ɗan wasan Najeriya da ya fi zura kwallaye a gasar cin kofin duniya ta FIFA.
Haka kuma, ya samu girmamawar jagorantar tawagar ƙasa a matsayin kyaftin, inda ya kasance jagora nagari a fili da kuma bayan fage, yana nuna koyi da jajircewa ga kasa da wasanni.
Ritayar Ahmed Musa ta kawo karshen wani zamani mai muhimmanci a tarihin tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, yayin da magoya baya, ’yan wasa da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa ke yabawa da gudunmawarsa, jagorancinsa da kuma gagarumin tarihin da ya bari a wasannin ƙwallon ƙafa na Najeriya.













































