Yanzu Yanzu: ASUU tace za ta daukaka kara kan umarnin janye yajin aiki da kotu ta ba su.

ASUU leader
ASUU leader

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ce ta shirya daukaka kara kan umarnin da kotun masana’antu ta ba su na dakatar da yajin aikin da ta kwashe watanni bakwai tana yi.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar shiyyar ikko, Adelaja Odukoya, yace kungiyar ta bukaci mambobinta da su kwantar da hankalinsu gameda wannan umarni.

Kungiyar ta ce tuni lauyanta ya shigar da kara akokarin bin kadin wannan umarni.

Sanarwar tace; “Ku kwantar da hankalinku.” Ta kuma bukaci mambobin kungiyar da ‘yan Najeriya da su kasance masu hadin kai, duk da cewa za a janye wannan umarni.

Sanarwar ta kara da cewa; “Shugaban kungiyarmu, Kwamared Victor Osodeke, ya bukaci mambobin kungiyarmu ta kasa da su kwantar da hankalinsu domin babu wani abin damuwa a bayan aiki da aka gabatar a yau.

“Lauyan mu ya shigar da kara dan dakatar da aiwatar da wannan hukuncin. Ba za a taɓa yin galaba a kan jama’ar da ke haɗin kai ba tare da sulhu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here