Majalisar Shari’a ta yi karin bayani kan buƙatar tsige shugaban INEC da gurfanar da shi gaban shari’a

INEC Chairman Joash Amupitan

Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya SCSN ta yi karin bayani kan kiran da ta yi na tsige Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, tare da gurfanar da shi gaban shari’a, inda ta bayyana cewa matsayarta ba ta ta’allaka ne kan addini ba, sai dai kan damuwa da haɗin kan ƙasa, mutuncin hukumomi, da kuma nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora.

A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar a ranar Litinin, wadda babban sakataren majalisar, Malam Nafi’u Baba-Ahmad, ya sanya wa hannu, majalisar ta ce matsayar ta biyo bayan shawarwarin da aka cimma a taron ta na shekara-shekara kafin watan Ramadan da kuma babban taron ƙungiyar, wanda aka gudanar a ranar 28 ga Janairu 2026 a Jihar Kaduna.

Majalisar ta bayyana cewa matsayar da ta dauka tun da farko ta haifar da martani daga jama’a da dama, inda wasu suka karkatar da fahimtar ta tare da fitar da ita daga ainihin ma’anarta, lamarin da ya sa aka ga dacewar yin wannan karin bayani.

Sanarwar ta ce kiran tsige shugaban INEC ya samo asali ne daga abin da majalisar ta bayyana a matsayin babbar damuwa kan tarihin baya da kuma ra’ayoyin da aka jingina wa Farfesa Amupitan a bainar jama’a, waɗanda ta ce na iya raunana tsaka-tsakin da ake tsammani daga shugaban hukumar zaɓen ƙasa.

Majalisar ta jaddada cewa addini bai taɓa zama sharadi ba wajen karɓa ko ƙin amincewa da shugabancin hukumomin zaɓe a Najeriya, inda ta nuna cewa yawancin mutanen da suka shugabanci hukumomin zaɓen ƙasar tun bayan samun ‘yancin kai Kiristoci ne.

Ta bayyana cewa daga cikin shugabanni 13 da suka jagoranci hukumomin zaɓe a Najeriya, biyu kacal Musulmai ne, kuma Musulman Najeriya ba su taɓa adawa da wani shugaban hukumar zaɓe saboda addini ba.

Sai dai majalisar ta nuna damuwa kan wata takardar shari’a da aka ce Farfesa Amupitan ya rubuta a 2020, wadda ta ce ta ƙunshi kalamai masu nuna son kai kan Musulman Najeriya, Daular Khalifanci ta tarihi, da Arewacin Najeriya.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa majalisar ta yi suka musamman kan zargin kisan kiyashi ga Kiristoci da kuma yunƙurin danganta matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya da jihadin ƙarni na 19 da Sheikh Uthman dan Fodio ya jagoranta, inda ta bayyana irin waɗannan ikirari a matsayin marasa tushe a tarihi kuma masu barazana ga zaman lafiya.

Ta kuma yi zargin cewa gabatar da irin waɗannan ikirari ga wasu ƙasashen waje ya nuna Najeriya ta fuskar da ba ta dace ba, tare da yiwuwar janyo matsin lamba daga waje bisa labaran ƙarya.

Majalisar ta ƙi amincewa da zargin kisan kiyashi ta fuskar addini, tana mai jaddada cewa tashin hankalin da ake fama da shi a Arewacin Najeriya yana da sassa da dama, ciki har da ta’addanci, fashin daji, aikata laifuka, talauci, matsalolin shugabanci, da rashin adalcin zamantakewa.

Majalisar ta kuma nuna damuwa kan yadda Farfesa Amupitan bai musanta rubuta takardar da ake zargi da shi ba, kuma bai fitar da neman afuwa ko janye kalaman ba, tana mai cewa hakan ya tilasta wa gwamantin tarayya yin martani a matakin diflomasiyya da kuma asarar kuɗi.

Sanarwar ta ce majalisar na ganin cewa irin waɗannan abubuwa sun ɓata sunan Najeriya a idon duniya, kuma suna bukatar daukar matakan kundin tsarin mulki da na shari’a idan ya zama dole.

Haka kuma majalisar ta yi kira ga al’ummar Kiristoci a Najeriya da su guji fadawa tarkon labaran rarrabuwar kai, yayin da ta sake tabbatar da kudirin al’ummar Musulmi na zaman lafiya, mutunta juna, da kare haƙƙin dukkan ‘yan Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here