Kogi: ƴan sanda za su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙungiyar Lauyoyi domin inganta tsaron jama’a

WhatsApp Image 2025 12 03 at 21.44.29 1 750x430

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kogi, Naziru Bello Kankarofi, ya bayyana cewa rundunar ƴan sandan jihar za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙungiyar lauyoyi NBA ta Najeriya reshen Lokoja domin ƙarfafa adalci, bin doka, da kare lafiya ta hanyar inganta aikin ƴan sanda.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar shugabannin ƙungiyar a ranar Laraba, kamar yadda kakakin rundunar, William Ovye Aya, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta bayyana cewa kwamishinan ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da masana harkar shari’a tare da tabbatar da gaskiya, ƙwarewa da haɗin kai ba tare da lamunce wa aikata kuskuren aiki ba.

Ya kuma yaba da muhimmiyar rawar da ƙungiyar ke takawa wajen taimakawa gudanar da shari’ar laifuka, tare da ƙarfafa ta da ta ci gaba da ziyarar wuraren tsare mutane domin duba yanayi.

Haka kuma ya jaddada bukatar musayar bayanai da haɗin kai domin hana aikata laifi.

Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya reshen Lokoja, AS Abbas, ya yaba da irin ƙoƙarin da ƴan sanda ke yi wajen yaki da aikata laifuka a jihar, tare da jaddada muhimmancin ƙara haɗin kai tsakanin rundunar ƴan sanda da ƙungiyar.

Ya kuma tabbatar da cewa suna da niyyar ci gaba da aiki tare da rundunar domin inganta gudanar da adalci.

Sanarwar ta ƙara bayyana cewa ziyarar ta kasance wata muhimmiyar dama da za ta ƙarfafa ingantaccen tsarin shari’a da samar da ƙarin tsaro ga al’ummar jihar Kogi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here