Da ɗumi-ɗumi: Yadda ɗalibai ƴan mata 25 da aka sace a Kebbi suka shaƙi iskar ƴanci

Kidnapped Kebbi School Girls Regain Freedom 750x430

Ɗalibai ƴan mata 25 da aka sace daga Makarantar sakandare a Maga da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi sun shaƙi iskar ’yanci ta hanyar amfani da dabarun lumana da gwamnatin tarayya ta aiwatar.

Rahotanni sun nuna cewa sakin ɗaliban ya faru ne sakamakon haɗin gwiwar jami’an Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro da Hukumar Tsaro Ta Ƙasa, wadanda suka jagoranci aikin cikin tsari da bin matakan nsasanci.

An yi amfani da wannan dabarar ba tare da amfani da ƙarfin soja ba, lamarin da ya nuna sauyin tsarin gwamnati na magance manyan garkuwa da mutane ta hanyar tattaunawa da gina amincewa domin kare rayukan fararen hula.

Ƴan bindiga sun mamaye makarantar kwana da ke Maga ne a ranar Litinin, 17 ga Nuwamba, inda suka yi awon gaba da ɗaliban a wani lamari da ya tayar da hankula a sassan ƙasa.

Sace ɗaliban ya biyo bayan wasu hare-haren makamancin haka a yankin, wanda ya sa hukumomin tsaro tsananta bincike da sanya dakarun ƙasa cikin hanzari domin gano inda aka kai su da kuma tabbatar da ceto cikin aminci.

Sakin ɗaliban ya kawo babban sauƙi ga iyalansu da al’ummar yankin, waɗanda suka shnnafe kwanaki a cikin matsanancin damuwa tun bayan aukuwar lamarin.

A halin yanzu, hukumomin tsaro na ci gaba da sa ido da ɗaukar matakan kariya domin tabbatar da cewa irin wannan lamari ba zai sake faruwa ba a yankunan da ake kallon suna da rauni wajen tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here