Na karba, kuma na biya Dala miliyan 3m a asusun kamfanin Aisha Achimugu – shedun EFCC

Aisha Achimugu

A kotun tarayya da ke Abuja, wani shaidar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), mai suna Trinity Usman, ya bayyana cewa ya karɓa see kuma ya tura dala miliyan uku cikin asusun kamfanin Aisha Achimugu mai suna Oceangate Engineering Oil and Gas Limited.

Shaidar, wanda yake ɗan kasuwa a harkar canjin kuɗi (BDC), ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da shari’ar daraktar babban bankin SunTrust, Halima Buba, da abokin aikinta Innocent Mbagwu, bisa zargin taimakawa wajen safarar kuɗi har zuwa dala miliyan 12.

Hukumar EFCC ta gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhuma shida, bisa zargin gudanar da manyan mu’amalolin kuɗi ba tare da bin tsarin cibiyar kuɗi ba, wanda ya sabawa dokar hana safarar kuɗi ta shekarar 2022.

Usman ya ce wata hulɗa ta kasuwanci ce ta haɗa shi da Suleiman Ciroma, wanda ya nemi ya tura masa dala miliyan uku zuwa kamfanin Achimugu a watan Afrilu 2025.

Ya bayyana cewa kuɗin ya fito daga asusun kamfaninsa na Triple A and Tee Oil and Gas Nigeria Limited, kuma ya raba biyan a matakai huɗu.

Shaidar ya ƙara da cewa kamfaninsa na Triple A and Tee Bureau De Change Limited bai shiga cikin wannan mu’amala kai tsaye ba saboda lasisin kamfanin ya dakata a lokacin.

Ya ce ma’aikatansa biyu ne suka karɓi kuɗin daga Ciroma kafin a tura su zuwa asusun kamfanin Achimugu.

Lokacin da lauyoyin masu kare su Buba da Mbagwu suka yi masa tambayoyi, shaidar ya tabbatar da cewa bai sanar da su cewa lasisin kamfaninsa ya dakata ba, kuma ya yanke shawarar amfani da asusun kamfanin mai suna Oil and Gas ne saboda shi ne yake da kuɗin a lokacin.

Shaidar ya kuma amince cewa ya samu riba daga wannan mu’amala, amma bai taɓa sanin ko yin magana da waɗanda ake tuhuma ba. Bayan kammala tambayoyin lauyoyi, alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 10 da 11 ga watan Disamba domin ci gaba.

A zaman da ya gabata, wani shaidar hukumar EFCC, Suleiman Ciroma, ya bayyana cewa Aisha Achimugu ta nemi a tura kuɗin ne saboda ba za ta iya ajiye su a banki kai tsaye ba, don kauce wa tsaiko wajen yin canjin kuɗin da ta ke bukata domin sayen rijiyoyin mai guda biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here