Dole ne a bincika zargin lalata tsakanin Sanata Natasha da Akpabio – Amnesty

f4ffa387 8db6 421f 9c50 4217df18fefc.jpg

Ƙungiyar kare haƙƙi ta duniya Amnesty International ta ce ya zama wajibi a bincika zarge-zargen da Sanata Natasha Akpoti ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio na neman yin lalata.

Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta zargi shugaban majalisar da tauye wa sanatan haƙƙin wakiltar jama’ar mazaɓarta na jihar Kogi sakamakon matakin majalisa na dakatar da ita tsawon wata shida kan rashin ɗa’a ga majalisa.

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar a Najeriya ya fitar, Isa Sanusi ya ce: “Amnesty na kira ga mahukuntan Najeriya da su fara gudanar da sahihin bincike cikin gaggawa game da zargin lalata da Natasha ta yi wa Akpabio.

“Girman zargin ɗaya ne daga cikin dalilan da za su sa a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma sahihi.

“Idan hukumomin Najeriya suka gaza bincika wannan zargi zai jawo matsala mai girma, ciki har da kawo tsarin da zai dinga hana waɗanda aka ci zarafi ta hanyar lalata samun adalci.”

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here