Jami’ar Bayero ta kaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i don amfanin dalibai

BUK Senate
BUK Senate

 

Shugaban jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas a ranar Alhamis ya kaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i na zamani a sashin kula da harkokin dalibai da nufin horar da dalibai koyon dinki da kwalliya domin dogaro da kai bayan kammala karatunsu.

Solacebase ta ruwaito cewa Farfesa Sagir Abbas  ya ce shirin wani bangare ne na alkawurran da ya dauka na inganta jin dadin daliban jami’ar.

Shugaban jami’ar ya ce manufar ita ce a taimaka wa daliban su samu su koyi sana’o’in zamani da za su taimaka musu da abin da za su yi rayuwa kafin su samu aikin yi bayan kammala karatunsu.

Ya ce idan aka yi la’akari da mahimmanci, zai zama tushen samun kudaden shiga da kuma samar da ayyukan yi tun da gwamnati ba za ta iya samar da isasshen aikin yi ga matasa masu tasowa ba.

“Yau wani muhimmin ci gaba ne a gare ni yayin da Jami’ar ke shaida wani gagarumin ci gaba na inganta jin dadin dalibai ta hanyar dandali na samun kwarewa.

Wannan ya zo ne kawai watanni biyu bayan da Jami’ar ta kaddamar da wani shirin aiki wanda ya dauki dalibai 125 aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi,” Mataimakin Shugaban Jami’ar ya jaddada.

Ya ce, tuni daliban suka fara jin dadin albashinsu, ya kara da cewa bisa la’akari da tantancewar suna aiki yadda ya kamata,’’ in ji mataimakin shugaban jami’ar.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kayayyakin da aka tanada cikin adalci tare da yin amfani da lokacinsu yadda ya kamata wajen koyo ta yadda bayan kammala karatunsu za su rika tunawa da Jami’ar wajen bayar da ilimi da dabarun kasuwanci.

Ya yabawa shugaban cibiyar, Farfesa Shamsuddeen Umar bisa kafa cibiyar da kuma misalta halayensa na jagoranci da suka shafi inganta walwala ga dalibai.

A nasa jawabin, shugaban cibiyar, Farfesa Shamsuddeen Umar ya nuna godiya ga shugaban jami’ar da ya fara gudanar da irin wadannan ayyuka da ake yabawa, inda ya bayyana cewa za a ci gaba da yaba wa kokarin Farfesa Abbasa na har abada.

Mataimakiyar , Dakta Maryam Liman, ta umurci daliban da su yi amfani da wuraren da ake amfani da su wajen koyon sana’o’i daban-daban, inda ta ce hakan zai kasance abin dogaro a rayuwarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here