Nasiru Abdullahi wanda aka fi sani da Chile Maidoki ya mika kan sa ga rundunar yan sandan jihar Kano, sakamakon yana daya daga cikin yan daba uku da yan sandan Kano suke neman ruwa a jallo.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa Chile Maidoki wanda yake a Layin Falwaya Kurna, na daya daga cikin yan daba uku da rundunar yan sandan Kano tasa kyutar N100,000 ga duk wanda ya fadi inda suke a fadin kasar nan.













































