Yan bindiga sun halaka fiye mutum 30 a Sokoto’

bandits
bandits

Yan bindiga sun far wa ƙauyukan Raka da Bilangawa da Tudun Anga a yankin ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto da ke arewa maso yamacin Najeriya.

Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa akalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar lamarin. Mazauna ƙauyukan sun shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun yi wa ƙauyukan ƙawanya a ranar Asabar da rana inda suka riƙa buɗe wa al’umma wuta.

Wani mazaunin ƙauyen Raka da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa maharan sun je kauyen Raka a kan babura inda suka yi wa kauyen kawanya tare da buɗe wuta.

”A ƙauyen Raka sun kashe mutum 14, sannan cikin garin Bilingawa sun kashe mutum 18, sai garin Raka ƙarama inda aka kashe musu mutum biyu, sai garin Tudun Anza sun kashe mutum biyu, shi ne abin da ya kawo adadin mutanen da aka kashe a ƙauyukan ya kai mutum 36”, kamar yadda wani mazaunin ƙauyen Raka ya bayyana wa BBC.

Shi ma wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa BBC cewa yanzu haka ana cikin zaman ɗar-ɗar a ƙauyukan da ke maƙwabtaka da ƙauyukan da lamarin ya faru.

BBC ta tuntuɓi kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ASP Ahmad Rufai, wanda ya ce ba shi da cikakken labarin abin da ya faru, sai dai ya ce zai yi wa BBC ƙarin bayani da zarar ya kammala tattara bayanai game da harin.

Hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya na yunkurin dawowa bayan da a baya suka ɗan lafa.

Ko a ranar Asabar da safe ma rahotonni sun ce an sace wasu ƙananan yara fiye da 30 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here