Kotu ta soke dokar da ta hana shan wiwi a Uganda

1683392414298
1683392414298

Kotun tsarin mulki a Uganda ta soke dokar da ta haramta amfani da muggan kwayoyi, irin su tabar-wiwi da ganyen khat.

Hakan dai ya biyo bayan kalubalen da kungiyar manoman ganyen khat ta soma yi na tsawon shekaru shida da suka gabata a matsayin martani ga dokar shekarar 2015.

Yanzu dai an soke dokar baki-ɗaya bayan da kotu ta ce an zartas da shi ba tare da samun rinjaye ƴan maajlisa da ake bukata a majalisar.

Kafin a yi muhawara da kuma zartar da doka a majalisar dokokin Uganda, dole ne akalla kashi ɗaya bisa uku na dukkan mambobin da ke da hakkin kaɗa kuri’a su kasance a majalisar.

Ko da yake an soke dokar a yanzu, duk da haka akwai haɗarin cewa za a kama masu noma da sha ko kuma sayar da haramtattun kwayoyi a ƙarƙashin wasu dokokin Uganda.

A Uganda, jami’an tsaro sun kasance suna kai samame tare da ƙona gonakin da ake nome tabar-wiwi ko kuma ganyen khat.

A duk faɗin Afirka, ƙasashe suna yin yunƙuri don halatta kasuwanci da kuma fitar da tabar wiwi.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here