Sarkin Kano Aminu Ado ya fitar da jadawalin hawan Sallah, ya sanar da hukumomin tsaro

Aminu Ado Bayero sabo sabo

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da hukumomin tsaro shirye-shiryen gudanar da bukukuwan yawan Sallah na shekarar 2026 da za a yi a fadar sarki da ke Nasarawa a Kano.

A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 7 ga Maris, 2026 wadda aka aike wa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, majalisar masarautar Kano ƙarƙashin Bayero ta bayyana cewa an yi sanarwar ne domin tabbatar da samar da isasshen tsaro yayin bukukuwan gargajiya da ke nuna ƙarshen watan Ramadan da kuma bikin Eid al-Fitr.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wasiƙar, wadda sakataren sarkin na musamman Abdullahi Haruna Kwaru ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa sarkin da membobin majalisar masarautar sun amince da shirin abubuwan da za a gudanar a bukukuwan Sallah.

Abubuwan da za a gudanar sun haɗa da Hawan Sallah, Hawan Daushe, Hawan Nasarawa da Hawan Panisau tare da sauran wasannin al’adu.

Bisa jadawalin da fadar ta fitar, ayyukan ranar Sallah za su fara da jerin gwanon sarauta daga fadar sarki zuwa filin sallar idi, sannan a gudanar da sallar idi da huduba.

Bayan sallar, sarkin zai jagoranci jerin hawan doki na gargajiya tare da hakimai da jami’an fadar sarki.

Daga baya a ranar, sarkin zai karɓi gaisuwar masu sarauta, jami’an gwamnati da sauran jama’a a fadar sarki.

A washegari, ranar Asabar 21 ga Maris, za a gudanar da Hawan Daushe inda sarkin zai zagaya manyan titunan birnin tare da hakimai da dogaran fadar kafin ya dawo fadar.

A ranar Lahadi 22 ga Maris kuma, za a ci gaba da bukukuwan da Hawan Nasarawa, wani tsohon durbar da ake gudanarwa a yankin Nasarawa na tsohon birnin Kano.

Fadar ta kuma nuna godiya ga hukumomin tsaro bisa haɗin kan da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a lokacin bukukuwan tare da addu’ar samun Sallah cikin lumana a faɗin jihar.

Hawan sallah a Kano na daga cikin manyan bukukuwan al’adu a arewacin Najeriya, inda dubban mazauna gari da baƙi ke taruwa domin kallon hawan doki, kayan al’ada da kuma jerin gwanon sarauta.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takaddama kan shugabancin masarautar Kano bayan mayar da Muhammadu Sanusi II kan sarauta da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi, lamarin da ya haifar da rikicin doka da siyasa a jihar.

Duk da wannan rikici, fadar sarkin Aminu Ado Bayero na ci gaba da gudanar da ayyukan gargajiya daga fadar Nasarawa yayin da ake jiran sakamakon ƙarshe na shari’o’in da ke gudana kan shugabancin masarautar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here