Ƴan sanda sun tabbatar da kama matar da ake zargin ta kashe mijinta kwanaki kaɗan da auren su

Wife allegedly stabs husband to death 3 days after wedding 750x430

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da cafke wata sabuwar amarya da ake zargin ta kashe mijinta bayan kwana uku kacal da ɗaurin aurensu a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa an samu rahoto cewa an tarar da angon cikin jini a gidansa dake unguwar Tashar Buja, inda daga bisani aka garzaya da shi asibiti, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa an tarar da mamacin da rauni mai zurfi a wuyansa, lamarin da ya sa ’yan sanda suka tura jami’an bincike zuwa wurin domin tattara hujjoji da gano musabbabin faruwar lamarin.

Rundunar ta tabbatar da kama matarsa da ake kyautata zaton ita ce ta kashe shi, wadda yanzu haka take tsare yayin da bincike ke ci gaba domin gano hakikanin abin da ya faru tsakanin ma’auratan.

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa marigayi, Abubakar Abdulkarim wanda aka fi sani da Dan Gaske, ya auri matar ne a ranar Alhamis, kafin a tsinci gawarsa a ranar Lahadi da rana a cikin gidansu.

Wasu maƙwabta na yankin sun ce amaryar ta je neman abinci a gidan makwabta, abin da ya jawo shakku, lamarin da ya sa suka koma gidanta inda suka tarar da mijinta kwance ba shi da rai.

Iyayen mamacin sun musanta jita-jitar cewa an tilasta musu aure, suna mai cewa ma’auratan sun kasance cikin kyakkyawar mu’amala kafin wannan abin takaici ya faru.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Katsina, CP Bello Shehu, ya tabbatar wa jama’a cewa ana gudanar da bincike cikin tsanaki, tare da roƙon duk wanda ke da wani muhimmin bayani da zai taimaka a binciken ya sanar da hukuma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here