Ƴan sanda sun kama wata tawagar masu fashi da makami a hanyar Katsina zuwa Kano

IMG 20251015 WA0012 1 652x430

Hedikwatar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta ce ta kama wata tawaga ta mutane 11 da ake zargi da aikata fashi da makami a manyan hanyoyin Sha’iskawa–Charanchi da Katsina zuwa Kanki zuwa Kano.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewa waɗanda ake zargin sun kware wajen tare manyan hanyoyi suna kwace dukiya daga hannun masu motoci ba tare da sani ba.

Ya ce rundunar ta samu nasarar kama su ne bayan samun bayanan sirri daga al’umma, inda aka kaddamar da samame da ya kai ga cafke su.

Rundunar ta kuma ce waɗannan mutane sun dade suna addabar masu amfani da hanyar, suna satar motocci da kayayyaki.

DSP Aliyu ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da: Dikko Maaru, Dardau Kabir, Muntari Musa, Labaran Amadu, Usman Maaru, Lawal Zubairu, Nasiru Sanusi, da Adamu Kabir, tare da wasu da ake ci gaba da bincike a kansu.

Rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mambobin ƙungiyar da ke gudun hukunci, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a laifin zai fuskanci hukunci mai tsanani.

‘Yan sanda sun tabbatar wa jama’a da cewa za su ci gaba da yin aiki ba dare ba rana domin tabbatar da tsaro a dukkanin manyan hanyoyin jihar da maƙwabtansu, musamman a tsakanin Katsina da Kano, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here