Ƙungiyar likitoci ta NARD ta janye yajin aikin da ta tsunduma

Doctors NARD 750x430

Likitocin masu neman ƙwarewa a Asibitin University College Hospital UCH da ke birnin Ibadan, za su koma bakin aiki da ƙarfe 8:00 na safiyar gobe Laraba bayan dakatar da yajin aikin gama gari a faɗin Najeriya da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa NARD ta janye.

Shugaban ƙungiyar likitocin ARD na asibitin UCH, Uthman Adedeji, ne ya tabbatar da hakan a yau Talata a ganawarsa da kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, inda ya ce, mambobinsu za su bi umarnin da aka bayar a matakin ƙasa.

An dakatar da yajin aikin ne bayan taron gaggawa na Majalisar zartarwar ƙungiyar ta ƙasa, wanda ya umarci likitocin su koma bakin aiki, bayan gwamnatin tarayya ta janye matakinta kan tsarin sabon alawus-alawus da kuma alƙawarin magance sauran matsalolin da suka jawo taƙaddama.

Sai dai kafin cikakken komawar aiki, Adedeji, ya bayyana cewa ba za a karɓi sabbin marasa lafiya ba har zuwa safiyar gobe Laraba, domin bai wa likitoci damar miƙa marasa lafiya da ke hannunsu ga manyan likitoci yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa za a sallami marasa lafiya masu sauƙin jinya, yayin da za a kula da masu matsanancin hali bisa izini na musamman, domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Ya kuma jaddada kudirin likitocin na ci gaba da kula da marasa lafiya, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta cika sauran buƙatun domin kauce wa sake komawa yajin aiki a fannin lafiya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here