Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe Hakimin Maigari a karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano, Alhaji Dahiru Abba.
Sabon babban sakataren shari’a na jihar Kano, Alhaji Sanusi Abbas, wanda kuma dan gidan marigayin ne ya tabbatar da faruwar lamarin, ga Jaridar Justice Watch.
Ya ce marigayi Hakimin Kauyen uba ne ga shugaban karamar hukumar Rimin Gado na yanzu Barista Munir Dahiru Maigari.
A cewarsa, Marigayi Maigari ya rasu ne bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa gidansa hari da sanyin safiyar Lahadi, inda suka yi masa raunuka daban-daban daga bisani suka harbe shi har lahira.
Ya bayyana cewa za a gudanar da Sallar jana’izar a yau a gidansa da misalin karfe 10 na safe a kauyen Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano.
Sai dai har izuwa yanzu rundunar ‘yan sandan Kano ba ta ce uffan kan lamari ba.













































