Yadda ake zargin Ganduje ya karkatar da hannun jarin Kano a tashar Tsandauri

Ganduje sad 750x430

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kwace hannun jarin kashi 20 cikin 100 na gwamnatin jihar a kamfanin Dala Inland Dry Port Nigeria Limited, ya kuma mayar da shi hannun jarin ’ya’yansa kafin ya bayar da kwangilar sama da naira biliyan hudu don gina ababen more rayuwa a wurin.

Wannan mataki ya hana gwamnatin jihar ikon mallakar tashar, inda aka sanya ’ya’yan Ganduje cikin daraktoci da masu hannun jari na kamfanin.

Tun da farko, gwamnatin jihar Kano ta mallaki kashi 20 na hannun jarin kamfanin tun shekarar 2006 a zamanin Malam Ibrahim Shekarau.

Bisa tsarin gwamnatin tarayya na wancan lokaci, an tsara mallakar tashoshin ruwa da rarraba hannun jari ga gwamnati da masu zaman kansu.

Sai dai rahotanni sun nuna ba Shekarau ba, ba kuma Rabiu Kwankwaso da ya gaje shi ba ne suka aiwatar da ayyukan ababen more rayuwar da gwamnatin jihar ta dauki alkawarin samarwa.

Rahotanni sun bayyana cewa rashin ci gaban aikin ya sa hukumar kula da masu jigilar kaya ta Najeriya (Shippers’ Council) ta yi barazanar soke kwangilar aikin a shekarar 2019.

Daga bisani, rahotanni suka nuna cewa dan kasuwa Ahmad Rabiu ya mika kaso 60 na hannun jarinsa ga iyalan Ganduje domin kauce wa soke kwangilar, wanda hakan ya bai wa iyalan tsohon gwamnan damar shiga cikin shugabancin kamfanin.

Bayan haka ne Ganduje, a matsayinsa na gwamnan jihar, ya bayar da kwangilar sama da naira biliyan 2.3 a shekarar 2020 ga kamfanin FRI Construction don gina hanyoyi, katanga, da sauran ayyuka a tashar.

Kwangilar daga baya ta karu zuwa sama da naira biliyan hudu, duk da cewa a wancan lokaci gwamnatin Kano ba ta kasance cikin masu hannun jari ba.

Bincike ya gano cewa daga baya aka cire gwamnatin jihar daga cikin masu hannun jari, aka sanya ’ya’yan Ganduje da abokin siyayarsa, Abubakar Bawuro, a matsayin daraktoci da masu hannun jari.

Daga bisani, an sake sauya tsarin mallaka, inda Bawuro ya mallaki kashi 80 cikin 100 na hannun jari, yayin da Rabiu ya rike kashi 20.

Sai dai gwamnatin Jihar Kano ta hannun gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, ta ce ba ta taba siyar da hannun jarinta a tashar ba.

Ta kuma bayyana cewa a hukumance har yanzu Kano na da mallakar kaso 20 na hannun jari, tare da shirin kara hannun jarin don habaka kudaden shiga.

Gwamnatin ta kuma ce tana gudanar da bincike kan yadda aka yi aka mallaki kaso mafi rinjaye ba tare da bin ka’ida ba.

Wannan rikici ya kunno kai ne shekaru bayan tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar a shekarar 2023, wacce aka ce yanzu haka tana aiki sosai.

Sai dai kwace hannun jarin Kano ya hana al’ummar jihar cin moriyar mallaka a tashar tsandauri ta Dry Port din.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here