Babban Sufeto janar na ‘yan sandan kasa Kayode Egbetokun ya bayyana cewa an dawo da jami’ai 11,566 daga aikin tsaron da suke baiwa mutane na musamman kariya na (VIP) domin aiwatar da umarnin shugaban kasa na janye ma’aikata daga tsaron mutum ɗaya.
Ya ce sake tura wadannan jami’an zuwa yankuna da ba su da isasshen tsaro ya fara ne domin karfafa aikin rundunar a wuraren da ake bukatar kariya sosai.
Kayode ya bayyana cewa wannan umarni daga shugaban kasa Bola Tinubu wani tsari ne da aka shirya don daidaita dabarun tsaro na kasa, bisa la’akari da yanayin tsaro na yanzu.
Sufeto janar din ya ce matakin yana karfafa aikin kare jama’a, tsaron al’ummomi da kiyaye dokoki a fadin kasa.
Ya kara da cewa janye jami’an daga tsaron mutane zai baiwa rundunar damar kara yawan sintiri, karfafa tsaron kauyuka da birane, fadada bincike da kuma dakile barazanar tashin hankali da ke tasowa.
Karanta: Yanzu-Yanzu: Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro, ya umarci a dauki sabbin Sojoji da ƴan sanda
A cewar sa, rundunar za ta fitar da cikakkun matakan aiwatarwa cikin tsari domin guje wa kuskuren fahimta ko amfani da wannan mataki wajen cimma muradin siyasa ko yaudara.
Sufeto janar din ya ce za a fara sanar da matakan cikin gida kafin a sanar da su ga jama’a ta hanyoyin da suka dace domin kare amincin tsarin.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci ta tsaro a fadin kasa tare da bada umarnin daukar karin ma’aikata a rundunar soji da ‘yan sanda saboda karuwar hare-hare da sace-sacen mutane.
Ya kuma umurci jami’an da aka janye daga tsaron VIP da su samu horo na gaggawa domin inganta aikinsu a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Ya amince da amfani da sansanonin NYSC a matsayin wurin horas da sababbin ma’aikatan tsaro domin tabbatar da cewa an samu karin jami’an da za su raya aikace-aikacen tsaron kasa yadda ya kamata.













































