Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kafa cikakken shingayen ta tsaro a dukkan dazukan Jihar Kwara sakamakon yawaitar sace mutane da hare-haren ’yan ta’adda da suka sake ƙaruwa a yankin.
Tinubu ya umarci rundunar sojin sama da ta faɗaɗa sintirin sama zuwa cikin lungu da saƙo na dazukan da ake zargin ’yan ta’adda suna ɓoye.
Umurnin shugaban ƙasar ya fito ne ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Ya ƙara da cewa wannan umarni ya shafi jihohin Neja da Kebbi ma, domin a tabbatar da ceto mutanen da ake tsare da su a yankunan.
A cewar Dare, an bukaci sojojin sama da su gudanar da sintiri na awanni 24 a sama domin tallafawa rundunonin da ke ƙasa wajen bincike da fatattakar ’yan ta’adda.
Karanta: Babu wani kuɗin fansa da aka biya domin ceto ɗaliban sakandaren Maga a Kebbi – Gwamna Idris
Gwamnati ta kuma roki al’ummomi da su rika bayar da sahihan bayani cikin gaggawa idan sun ga motsi ko al’amura masu ban shakka, domin taimaka wa jami’an tsaro.
Hare-haren da suka faru kwanan nan sun hada da farmakin da ’yan ta’adda suka kai makarantar St. Mary’s Catholic da sakandaren Papiri a Jihar Neja, inda aka yi garkuwa da fiye da dalibai da ma’aikata 300.
A cikin mako guda kuma, an sace ’yan mata 25 daga makarantar yan mata da ke Maga a Jihar Kebbi, tare da wasu masu ibada 38 da aka dauke daga coci a Eruku, Jihar Kwara.
Akalla mutane 50 daga cikin wadanda aka sace a makarantar St. Mary’s sun tsere daga hannun masu garkuwa, amma fiye da yara da mutane 265 har yanzu suna tsare.
Wannan lamari ya sake tunasar da al’umma bala’in sace daliban Chibok a shekarar 2014, inda har yanzu kusan dalibai 90 ba a gano su ba.
Gwamnati ta ce matsalar tsaro da ake fuskanta ta samo asali ne daga harin ’yan ta’adda da tawagar ’yan bindiga da ke kai farmaki kauyuka, sace mutane da neman kudin fansa.
Ta bayyana cewa matakan da ake ɗauka yanzu na nufin murkushe waɗannan kungiyoyi da dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.













































