Takarar Gwamna 2027: Ƴan Majalisa daga Kano sun goyi bayan Sanata Barau ya yi takarar Gwamna domin shi yafi dacewa

WhatsApp Image 2025 11 19 at 14.17.49 750x430

Wasu ƴan majalisar Dokokin Kano da tsofaffin ƴan majalisar sun bayyana goyon bayansu ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, domin takarar gwamnan jihar a shekarar 2027, bayan da suka kai masa ziyarar ban girma domin nuna cikakken goyon bayansu.

Sama da mutum dari biyu daga cikin yan majalisar tun daga daga 1999 zuwa yanzu karkashin jagorancin tsohon kakakinta Abdulaziz G. Gafasa sun hallara a wajen ziyarar, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya fi dacewa ya jagoranci jihar.

Wani bayani da mai bada shawara na musamman kan yada labarai ga mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Malam Ismail Mudashir, ya fitar ya nuna cewa suna kallon Sanata Barau a matsayin dan takara mafi karbuwa a jam’iyyar APC saboda irin ayyukansa a Abuja.

Ko da yake har yanzu Sanata Barau bai bayyana aniyarsa ta takara ba, jiga-jigan jam’iyyar APC a Kano na kara nuna goyon baya gare shi saboda rawar da ya taka a majalisar Tarayyar cikin shekaru goma da suka gabata.

Karanta: Sanata Barau ya karɓi ƴan NNPP Kwankwasiyya sama da 1,000 da suka sauya sheƙa zuwa APC a Kano

Tsohon kakakin majalisar ya ce sun tsaya tsayin daka a bayansa saboda yadda ya inganta rayuwar jama’a a mazabu uku na jihar, ya tallafawa jam’iyyar APC, tare da taimakawa mutane da dama duk da ba daga mazabarsa suke ba, lamarin da ya kara tabbatar da shi a matsayin dan takara mafi karbuwa.

Wani dan majalisar dokokin Kano, Garba Yau Gwarmai, ya bayyana cewa za su hada kai da al’umma domin mara masa baya a zaben 2027 saboda irin tasirin da ya yi wajen bunkasa Kano.

A nasa bangaren, Sanata Barau ya gode musu bisa goyon bayan da suka nuna masa, ya kuma bukace su da su ci gaba da hada kai domin dawo da martabar Kano tare da tabbatar da manufofin jam’iyyar APC da shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ciyar da jihar gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here