Sojoji sun kama wani da ake zargi da laifin yin garkuwa, daidai lokacin da yake tattaunawa kan Naira Miliyan 20 a matsayin kuɗin Fansa

The Suspect Mr. Umar Geyi 750x430

Dakarun Sojin ƙasar nan sun kama wani da ake nema saboda zargin garkuwa da mutane mai suna Umar Geyi, bayan da suka bi diddigin sa zuwa wani yanki a jihar Taraba, inda ake zargin ya nemi kuɗin fansa Naira Miliyan Ashirin domin sakin wanda ya yi garkuwa da shi, Alhaji Jano.

Geyi ya yi garkuwa da Jano, ɗan ƙabilar Fulani da ke zaune a yankin Jandei-Kulala, a ranar 13 ga watan Nuwamba, wanda ya jawo babban bincike da ya kai ga kama shi.

Mataimakin daraktan yada labarai na rundunar sojojin ƙasa ta Bataliya ta shida, Laftanar Umar Muhammad, ya bayyana cewa dakarun sashi na 3 na Operation Whirl Stroke tare da goyon bayan Operation Zafin Wuta ne suka gudanar da kamun a Jandei-Kulamu da ke ƙaramar hukumar Wukari.

Ya ce bayanan sirri sun nuna cewa an kama Geyi ne a ranar ashirin da biyu ga watan Nuwamba, kuma yana daga cikin manyan ‘yan bindigar da hukumomin tsaro ke nema saboda kasancewarsa cikin ƙungiyar masu garkuwa da ta addabi al’ummomi a yankin.

Karin labari: Hedikwatar tsaro ta musanta jita-jitar yunƙurin juyin mulki, ta tabbatar da biyayyarta ga Tinubu

Ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa Geyi na da hannu a garkuwa da Alhaji Jano wanda har yanzu yake a hannun masu garkuwa, kuma an kama shi ne yayin tattaunawar waya da ya tabbatar da cewa wanda aka sace yana raye tare da neman kuɗin fansa na Naira Miliyan Ashirin.

Hukumomin tsaro ba su kai ga gano wurin da ake tsare da Jano ba tukuna, inda ake ci gaba da tambayar Geyi domin gano inda yake tare da duba yiwuwar ceto shi cikin aminci.

Kwamandan rundunar Bataliya shida, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa dakarun bisa nasarar da suka samu, tare da nanata kudirin sojoji na ci gaba da murkushe masu garkuwa da mutane, da ceto waɗanda aka sace, da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su kasance cikin shiri tare da bayar da bayanan sirri cikin lokaci domin taimakawa ayyukan tsaro da ake gudanarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here