Sama Da ‘Yan Boko Haram Dari Da Hamsin Sojiji Suka Kashe Yau

Army new new 678x349 1
Army new new 678x349 1

Sama da ‘yan Boko Haram 150 ne suka rasa ransu a wani hari da sojijin saman Nigeria sukai kawai ‘yan kungiyar a dajin sambisa Kamar yadda wasu rahotanni suka tabbatar jirgin saman sojin Nigeria ya kai hari a ranar 21 ga watan Disambar wannan shekarar a wani sansanin ‘yan Boko Haram da ke Matari a karamar hukumar Bama ta jihar Barno.

Wata majiya a hukumar tsaron soji ta fadawa jaridar Zagazola cewa harin yayi mumunar illa ga maboyar ‘yan taddan da suke a yankin tafkin ChadZagazola.

cewa harin yayi mumunar illa ga maboyar ‘yan taddan da suke a yankin tafkin Chad.

Majiyar tace manyan kwamandojin kungiyar da suka hada da Babba Tukur, A kahid na cikin wanda suka rasa ransu yayin kai harin a sansanin Mantari da kuma na sansanin su na Maimusari.

Majiyar tace da ta samu wani kishin-kishin din kai harin ne bayan da ‘yan ta’addan suka gana da yan uwansu da suke zaune a Mantari, daga bisa ni suka karbi makamai da man mota suka koma. Su kuma sojojin sukai amfani da damar suka kai musu hari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here