Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP-GF) ta bukaci a kwantar da hankali da kuma nuna kame kai gabanin hukuncin da Kotun Daukaka Kara za ta yanke kan rikicin shugabancin jam’iyyar da ake sa ran yanke a yau Litinin.
Ƙungiyar gwamnonin na PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar dinsa, Dr Emmanuel Agbo ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
Agbo ya bukaci mambobin jam’iyyar, magoya baya da ma dukkan ‘yan Najeriya su kasance cikin natsuwa da ladabi a martaninsu ga hukuncin.
Ya ce martanin kowa dole ne ya nuna balaga da kuma girmama bin doka.
Ya kuma bukaci dukkan mambobin jam’iyyar da shugabanni su nuna cikakken kame kai, su kasance masu bin doka kafin hukunci, yayin hukunci da kuma bayan hukuncin.
Agbo ya ce shugabancin jam’iyyar zai gana nan take domin nazarin hukuncin tare da tsara matakan da za a dauka bayan hukuncin.
Ya ce ko wane irin hukunci aka yanke, jam’iyyar PDP na sake jaddada girmamawarta ga tsarin shari’a da kuma kudurinta na zaman lafiya.
Ya bayyana cikakken amincewar jam’iyyar ga bangaren shari’a wanda ya ce shi ne mai kula da adalci kuma ke da nauyin tabbatar da gaskiya, adalci da kuma kare zaman lafiyar kasa.
Ya kara da cewa yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027, jam’iyyar PDP na nan daram kan kudurinta na bai wa ‘yan Najeriya wata madadin siyasa mai karfi, sahihiya kuma mai mayar da hankali ga jama’a.
Ya kuma ce babu wani hukunci da zai iya goge muradin ‘yan Najeriya na tsarin siyasa mai gaskiya da kuma gasa.
Ya kara da cewa jam’iyyar a shirye take ta shiga gaba daya cikin tsarin dimokuradiyya domin tabbatar da cewa muryoyin jama’a an ji kuma an girmama su.
Ya ce bangaren shari’a shi ne bangaren gwamnati mafi nuna adalci ga jama’a, wanda kokarinsa na kare kundin tsarin mulki ya taimaka wajen tabbatar da dorewar dimokuradiyyar Najeriya.
Agbo ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP ta kasance ginshiki a tafiyar dimokuradiyyar Najeriya.
A cewar sa, jam’iyyar ta taba rike mulki, ta kasance a matsayin ‘yar adawa, kuma ta bada gudummawa wajen karfafa cibiyoyin da ke kare hakkin ‘yan kasa.
Ya kara da cewa dimokuradiyya na bunkasa ne ta hanyar bambancin ra’ayoyi, gasa ta tunani da kuma damar da ‘yan kasa ke da ita wajen zabar madadin shugabanci masu sahihanci.
Ya ce jam’iyyar PDP za ta ci gaba da rike wadannan dabi’u, saboda haka ta bukaci dukkan mambobin da ke da burin siyasa su shiga takarar babban zaben 2027 su kasance da yakini da cewa jam’iyyar na da dandali da zai tabbatar da nasararsu a zabe.
Har ma ya kara da cewa duk da cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta riga ta fitar da jadawalin babban zaben, jam’iyyar za ta tabbatar da karewa da kuma cikar burin siyasar su.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Kotun Daukaka Kara ta ajiye hukunci tun ranar 13 ga Fabrairu kan kararrakin daukaka kara guda tara da bangarori daban-daban na jam’iyyar PDP suka shigar dangane da babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan jihar Oyo a watan Nuwamba 2025.
Kararrakin sun samo asali ne daga hukuncin da alkalai biyu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja James Omotosho da Peter Lifu suka yanke
Haka kuma an samu wasu hukunci na daban daga Babbar Kotun Jihar Oyo da kuma Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan kan wannan taron jam’iyyar da ake takaddama a kansa.
Duk da hukuncin da ya dakatar da gudanar da taron kafin ranar da aka tsara, masu shirya taron sun ci gaba da gudanar da shi a Ibadan tsakanin 15 zuwa 16 ga Nuwamba 2025 inda aka zabi Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa tare da sauran jami’an kasa.
Akwai kuma wata kara mai alaka da wannan batu a gaban Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja wadda wani bangare na jam’iyyar da ke tare da ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike ya shigar domin hana bangaren Turaki wakiltar jam’iyyar da kuma hana Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Kasa DSS ba su damar shiga sakatariyar PDP da ke Abuja.
A ranar 23 ga Janairu mai shari’a Abdulmalik ta dage sauraron karar zuwa 20 ga Fabrairu domin jiran matakin Kotun Daukaka Kara kan kararrakin da suka shafi taron Ibadan.
Yayin sauraron kararrakin daukaka kara, lauyoyin bangaren Turaki sun roki kotu ta amince da kararrakin tare da soke hukuncin da ya soke taron jam’iyyar.
Sai dai lauyoyin wadanda ake kara ciki har da shugaban riko Mohammed Abdulrahman wanda bangarensa ke tare da Wike sun bukaci kotu ta yi watsi da karar tare da tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya.
Lauyan masu daukaka kara Chris Uche SAN ya ce karar ta kalubalanci hukuncin da mai shari’a Omotosho ya yanke a ranar 31 ga Oktoba 2025 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Ya yi jayayya cewa an yanke hukuncin ba tare da hurumin kotu ba kuma ya roki kotu ta yi watsi da korafin farko da aka shigar kan karar.
Ya kuma bukaci kotu ta soke hukuncin da umarnin da mai shari’a Omotosho ya bayar.
Sai dai lauyan wadanda ake kara daga na farko zuwa na uku Joseph Daudu SAN ya bukaci kotu ta tabbatar da korafe-korafen farko tare da yin watsi da karar daukaka kara.
Sauran lauyoyin wadanda ake kara ma sun bukaci kotu ta yi watsi da karar.













































