Gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ta amince da kafa tawagar Najeriya zuwa aikin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da ƙasar Amurka domin zurfafa haɗin kai wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar.
Malam Nuhu Ribadu, wanda shi ne mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa, shi zai jagoranci ɓangaren Najeriya a wannan aiki tare da goyon bayan tawaga mai ƙunshe da wakilai daga muhimman hukumomi na tsaro da tsarin manufofi.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis.
Wannan ci gaban ya biyo bayan muhimman tattaunawar da aka gudanar kwanan nan a birnin Washington, inda mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ya jagoranci wakilan Najeriya.
Tawagar ta ƙunshi ministan harkokin wajen ƙasar, Yusuf Tuggar, ministan kariya Abubakar Badaru, da ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo, tare da ministan kula da harkokin jin kai Bernard Doro, babban hafsan tsaro Janar Olufemi Oluyede, da babban daraktan hukumar leken asiri ta ƙasa Mohammed Mohammed, da babban sufeton ƴan sanda Kayode Egbetokun.
Idayat Hassan daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da Paul Alabi daga ofishin jakadancin Najeriya a ƙasar Amurka za su kasance a matsayin sakatariyar aikin.
Shugaba Tinubu ya umarci tawagar da ta yi aiki kafada da kafada da abokan aikinta na ƙasar Amurka domin tabbatar da aiwatar da dukkan kudirin haɗin gwiwar da aka cimma bisa tsari da ingantaccen tsarin gudanarwa.
NAN












































