NBA za ta kai ƙarar Kwankwaso ga ’yan sanda kan zargin tsoma baki a zaɓen shekarar 2019

Sen. Rabiu Musa Kwankwaso

Kwamitin zartarwa na ƙasa na ƙungiyar lauyoyi ta kasa NBA ya yanke shawarar rubuta takardar ƙorafi ga rundunar ’yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro masu alaka, kan wasu kalamai da aka bayyana a bainar jama’a da ke nuni da tsoma baki ko amfani da tasiri ba bisa ƙa’ida ba a harkokin shari’a, musamman waɗanda aka jingina wa tsohon gwamnan jihar Kano, injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wannan matsaya ta biyo bayan tattaunawar da kwamitin ya yi sakamakon hankalin jama’a da ya karkata kan wasu kalamai da aka ruwaito Kwankwaso ya yi, inda ya nuna cewa ya taɓa shiga hulɗa da alkalan kotun koli a lokacin shari’ar zaɓen gwamnan jihar Kano na shekarar 2019.

Kwamitin ya lura cewa irin waɗannan kalamai, ko an faɗe su kai tsaye ko ta hanyar ishara, na iya raunana amincewar jama’a ga ’yancin kai na bangaren shari’a da kuma sahihancin tsarin shari’ar zaɓe a Najeriya.

Haka kuma, kwamitin ya yanke shawarar cewa binciken da ake nema kada ya taƙaita ga zargin da aka jingina wa Kwankwaso kaɗai ba, sai ya shafi duk wani mutum da ya taɓa yin furuci ko ikirarin da ke nuna cewa ya yi tasiri ko ya nemi yin tasiri ko kuma ya samu damar shiga harkokin yanke hukunci na shari’a ba bisa ƙa’ida ba.

A yayin amincewa da wannan matsaya, kwamitin ya jaddada cewa ƙorafin ya shafi ikirari da kalaman da aka yi ne kawai, ba wai tabbatar da laifi ba.

Manufar ita ce a tabbatar da cewa irin waɗannan zarge-zarge masu nauyi sun fuskanci cikakken bincike na gaskiya da ƙwarewa.

Kwamitin ya bayyana cewa idan ikirarin ƙarya ne, to suna da hatsari kuma suna gurbata tsarin dimokuraɗiyya, don haka dole a yi watsi da su ƙwarai.

Idan kuma gaskiya ne, dole a ɗauki matakin ladabtarwa bisa doka.

Saboda haka, kwamitin ya umarci shugabancin ƙungiyar lauyoyi na ƙasa da ya shirya tare da miƙa takardar ƙorafi ga rundunar ’yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da suka dace, domin gudanar da cikakken bincike kan dukkan zarge-zargen tsoma baki a harkokin shari’a, da nufin kare ’yancin kai na kotuna da dawo da amincewar jama’a ga tsarin gudanar da adalci.

Ƙungiyar ta sake jaddada cikakken jajircewarta ga mulkin doka da ’yancin kai na bangaren shari’a, tare da tsayawa kan cewa babu wani mutum, komai matsayinsa ko tarihinsa na siyasa, da ya cancanci yin ikirarin da ke jefa shakku kan sahihancin kotuna ba tare da an bincika shi bisa doka ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here