Na yi hidima kuma ina farin cikin barin aiki – Farfesa Pate

Pate Umaru 750x430

Shugaban jami’ar tarayya ta Kashere mai barin gado a jihar Gombe Farfesa Umaru A. Pate, ya bayyana gamsuwarsa da wa’adin da ya yi, yana mai cewa ya cika burinsa kuma yana farin cikin barin aiki bayan ya yi wa jami’ar hidima gwargwadon iyawarsa.

Farfesa Pate ya bayyana hakan ne a yayin wani taron bankwana da aka shirya domin girmama shi a ɗakin taro na majalisar jami’ar, inda shugabanni da ma’aikatan jami’ar suka yi masa yabo bisa jagoranci da nasarorin da ya cimma a lokacin mulkinsa.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Umaru Pate shi ne shugaban jami’a na uku tun bayan kafuwar Jami’ar Tarayya ta Kashere a shekarar 2010 a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

A yayin gabatar da cikakken bayani kan shugabancinsa, Farfesa Pate ya bayyana muhimman nasarorin da aka samu a wa’adinsa, waɗanda suka haɗa da bunƙasar gine-gine, ci gaban harkokin ilimi, inganta walwalar ma’aikata, da kuma warware shari’o’in kotu da suka daɗe suna damun jami’ar.

Ya gode wa majalisar gudanarwa, shugabanci, ma’aikata da ɗalibai bisa haɗin kai da goyon bayan da suka ba shi a tsawon wa’adinsa, yana mai cewa haɗin kan dukkan masu ruwa da tsaki ne ya taimaka wajen cimma nasarorin da aka samu.

Taron ya kuma kasance cike da kalaman yabo masu taɓa zuciya daga manyan jami’an jami’ar, waɗanda suka bayyana Farfesa Pate a matsayin jagora mai hangen nesa, mai renon matasa da kuma mai haɗa kan jama’a, inda suka ce wa’adinsa ya ƙarfafa daidaito da martabar jami’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here