Majalisar dokoki ta fara nazari kan buƙatar ƙirƙirar sabbin jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278

national assembly 1

Majalisar dokoki ta ƙasa ta fara tattaunawa kan gyare-gyaren kundin tsarin mulki da za su iya kaiwa ga ƙirƙirar sababbin jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278 a faɗin ƙasar nan.

Mai ba mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan yaɗa labarai, Malam Isma’ila Mudashir, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja a ranar Juma’a.

Sanarwar ta rawaito cewa taron hadin gwiwa tsakanin kwamitocin majalisar dattawa da majalisar wakilai kan duba kundin tsarin mulki na shekara ta 1999 ya gudana a birnin Legas.

Sanata Barau I. Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki, ya ce majalisar za ta tabbatar da isar da farkon kundin gyaran ga majalisun dokoki na jihohi kafin ƙarshen shekara.

Ya bayyana cewa, aikin ya ɗauki lokaci mai tsawo tun shekaru biyu da suka gabata, inda aka gudanar da tarurruka, jin ra’ayoyi daga jama’a da ƙungiyoyi daban-daban, wanda hakan ya kai ga samun buƙatu 69 da suka haɗa da ƙirƙirar jihohi 55, da daidaita iyaka biyu, da ƙananan hukumomi 278.

Barau ya ƙara da cewa, ‘yan majalisa za su warware batutuwan da ke gaban su cikin wannan zama na kwanaki biyu tare da fatan samun nasara kafin lokacin ƙarshe.

Ya jaddada bukatar haɗin kai da kishin ƙasa wajen gudanar da aikin, yana mai cewa dole ne a guji bambance-bambancen ra’ayi ko ƙabilanci.

Ƙokarin gyaran kundin tsarin mulki a baya ya kan fuskanci cikas saboda rikice-rikicen siyasa da rashin jituwa tsakanin jihohi, musamman kan batun ikon mallakar albarkatu, ƙirƙirar jihohi da ikon ƙananan hukumomi.

Masu lura da harkokin siyasa sun ce wannan sabon yunƙuri na iya zama wata dama ta sake gina tsarin mulki mai ɗorewa, sai dai yawan buƙatun sabbin jihohi da ƙananan hukumomi na iya zama kalubale ga dorewar haɗin kan ƙasa da yadda ake gudanar da mulki.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here