Kungiyar likitoci ta NARD ta ayyana fara yajin aikin sai Baba-ta-gani a kasa baki daya

Doctors NARD 750x430

Kungiyar likitoci ta (NARD) ta sanar da fara yajin aiki na kasa baki daya ba tare da iyaka ba, sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus na kwararru.

Sakataren kungiyar na kasa, Shuaibu Ibrahim, ya bayyana hakan bayan kammala wani taron gaggawa na kwamitin zartarwa na kasa da aka gudanar ta yanar gizo a ranar Asabar.

Ya ce za a fara yajin aikin da karfe 12:00 na dare a ranar Talata, 7 ga watan Afrilu, 2026.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana zargin gwamnatin tarayya da tilasta wa likitoci sake shiga wani sabon yajin aiki.

Ya ce majalisar zartarwa ta samu bayani kan matakin gwamnati na cire tsarin professional allowance table, wanda suka dauka a matsayin abin takaici.

Bayan tattaunawa mai zurfi, majalisar ta yanke shawarar fara cikakken yajin aiki daga ranar da aka kayyade.

Rikicin ya samo asali ne daga yarjejeniyar da aka cimma tsakanin NARD da gwamnatin tarayya bayan yajin aikin da ya gudana a shekarar 2025.

Yarjejeniyar ta kunshi karin albashi da alawus ga likitocin zama, ciki har da kudin aikin kira, alawus na shif, karin kudin aiki a karkara da kuma biyan kudin ayyukan da ba na asibiti ba.

An tsara fara aiwatar da sabon tsarin a watan Janairu 2026, daga baya aka mayar zuwa Fabrairu, amma kungiyar ta ce yanzu gwamnati na shirin dakatar da shi gaba daya a watan Afrilu.

Kungiyar ta ce wannan mataki na tauye amincewa tare da karya yarjejeniyar da aka cimma a baya.

NARD na bukatar a janye wannan mataki nan take tare da biyan dukkan hakkokin da ake bin likitoci.

Ta kuma bukaci a biya bashin karin girma da na albashi a wasu cibiyoyi, da kuma kammala biyan kudin horas da likitoci na shekarar 2026.

Haka kuma ta dage kan a biya bashin watanni 19 na alawus na kwararru da ake bi.

Kungiyar ta bukaci mambobinta a fadin kasar nan da su kasance cikin hadin kai tare da tabbatar da cewa sun ci gaba da wannan mataki har sai an cimma bukatunsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here