Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Filin Hockey a Kano ta tura matasa masu tashe a TikTok ciki har da Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.
Ragowar wadanda kotun ta tisa keyarsu zuwa gidan yarin sun hada da babban abokin Murja Kunya, wato Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi wakar ‘A Daidaita’.
Hakan kuwa na zuwa ne a yayin da ita Murja take cika mako biyu da zaman wakafi a gidan yari.
A zaman kotun na ranar Alhamis ne Mai Shari’a Abdullahi Halliru, ya ba da umarnin tisa keyar masu amfani da TikTok din zuwa gidan yari.
Kotun ta tura su zaman wakafin na tsawon mako guda ne a shari’ar da zauren malaman Kano ta maka matasan kan zargin wallafa bidiyon batsa a TikTok.
Ana zargin Murja da abonkan nata ne da laifin yada batsa a TikTok, amma duk sun musanta zargin.













































