Jam’iyyar NNPP ta bukaci a gudanar da binciken gaggawa kan zargin karkatar da dukiyar kasa da Abba Ganduje, dan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda kuma ke dan takarar majalisar wakilai ne na jam’iyyar APC a Dawakin Tofa, Rimingado and Tofa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyar NNPP na jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya fitar a ranar Alhamis.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Doguwa a cikin sanarwar ya bayyana cewa, ta gano cewa gwamnatin jihar ta karkatar da motoci sama da talatin na hukumar tattara kudaden shiga ta kano zuwa ayyukan yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar APC.
Sanarwar ta ce, motocin da ke dauke da hoton Abba Ganduje an shirya raba su ne ga shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Rimingado, Tofa, da Dawakin Tofa na tarayya domin titsiye Tijjani Jobe wanda ya raba motoci kusan ashirin ga mambobin jam’iyyar a kwanan baya.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, an tattara motocin a harabar jami’ar wucin gadi ta Jami’ar Arewa maso Yamma Kano, kafin jiran lokacin rabon tallafin ga magoya bayan dan Gandujen, Abba, inji sanarwar.
“Don haka muna rokon hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFCC, ICPC da INEC da su binciki wannan almundahana da dukiyar kasa.”
“Gwamna Ganduje ya shahara wajan tafiyar da gwamnatin son zuciya da tsangwama ta hanyar tsoma iyalansa da yawa a cikin harkokin gwamnatin jihar, a matsayinmu na jiga-jigan ‘yan adawa, ba za mu ci gaba da yin shiru kan irin wannan wakaci-katashi da ake ba.” Doguwa ya tabbatar
Duk wani yunkurin da SOLACEBASE ta yi na jin ta bakin Abba Ganduje ya ci tura domin layin wayarsa ba ya tafiya, kuma bai amsa sakon karta-kwana da aka aika masa ba.













































