Iyalan mashahurin malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, sun tabbatar cewa za a gudanar da sallar jana’izar mamacin bisa ga wasiyya da ya bari sama da shekaru ashirin da suka wuce.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa Sheikh Dahiru Bauchi, ɗaya daga cikin mashahuran malamai a Najeriya, ya rasu da safe ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, bayan gajeren rashin lafiya.
Iyalan sun bayyana cewa mamacin ya bar wasiyya kan wanda zai jagoranci sallar jana’izarsa.
A wata tattaunawa da wakilin SolaceBase, ɗaya daga cikin ‘ya’yansa, Dr Abubakar Surumbai Dahiru Bauchi, ya bayyana cewa wannan umarni ya fara ne sama da shekaru 20 da suka wuce, bayan rasuwar ɗan uwan su, Dr Hadi Dahiru Bauchi.
Cikin wasiyyar, Sheikh Dahiru ya gaya wa iyalansa cewa ya riga ya baiwa marigayi yayan su Dr Hadi wasiyya, cewa idan ya rasu, Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh shi ne zai jagoranci sallar jana’izarsa.
Karin labari: Gwamnatin Kano ta nuna alhininta kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Ya tabbatar cewa iyalansa sun adana wannan umarni har zuwa yau da ya rasu.
Ya bayyana cewa tun da Sheikh ya ba su wannan wasiyya, sun riƙe ta, kuma sun sanar da Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh, wanda ya amince zai zo bayan sallar Jumu’ah gobe domin gudanar da jana’izar kamar yadda aka umarta.
Ya yi kira ga al’umma su kasance cikin natsuwa kuma su bi ƙa’idojin da mamacin ya koyar.













































