Gwamnatin Tarayya ta soke tsarin koyarwa da Harshen Uwa, ta ayyana Turanci a matsayin Harshe guda na koyarwa

Morufu Tunji Alausa 678x430

Gwamnatin tarayya ta soke manufar ƙasa da ta wajabta amfani da Harshen Uwa wajen koyarwa a makarantun ƙasar.

Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a taron kasa da kasa kan Harshe a fannin ilimi na shekarar 2025 da ƙungiyar British Council ta shirya a birnin Abuja ranar Laraba.

A shekarar 2022, gwamnati ta amince da wata manufa ta ƙasa kan Harshe wadda ta tanadi cewa daga matakin makarantar yara ƙanana zuwa ajin ƙarshe na firamare, koyarwa za ta kasance da Harshe na gida ko na al’umma mafi kusa.

Manufar ta kasance don inganta harsunan gida, tabbatar da matsayin su ɗaya, da kuma haɓaka fahimtar yara a matakin farko na ilimi, yayin da Turanci ke zama harshe na hukuma a matakai na gaba.

Yayin taron, Minista Alausa ya bayyana cewa daga yanzu Turanci ne kawai za a riƙa amfani da shi a matsayin Harshen koyarwa a dukkan matakan ilimi daga firamare har zuwa jami’a.

Ya ce daliban Najeriya sun yi ta faduwa a jarabawar ƙasa saboda amfani da Harsunan gida wajen koyarwa, inda bayanan bincike suka nuna cewa tsarin ya haifar da koma baya a sakamakon karatu a wasu yankuna.

Alausa ya kara da cewa bayanin da aka tattara daga makarantu a fadin ƙasa ya nuna cewa daliban da ake koyarwa da harsunan gida suna samun rashin nasara a jarabawar ƙasa kamar WAEC, NECO da JAMB, tare da matsalolin fahimtar Turanci.

Saboda haka, ya bayyana cewa an soke manufar ƙasa kan harshe gaba ɗaya, kuma Turanci ne yanzu zai zama Harshen koyarwa a dukkan matakan ilimi.

Ministan ya bukaci masu ruwa da tsaki da ke da ra’ayoyi daban su gabatar da hujjojin bincike don goyon bayan matsayinsu, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da bude kofa ga tattaunawa bisa hujja domin inganta tsarin ilimi.

Haka kuma, Ministar ƙasa da Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmed, ta bayyana cewa gwamnati ta ƙirƙiri sabon tsarin horas da malamai domin ƙarfafa koyon karatu da lissafi a matakin farko na ilimi.

Shugabar ƙungiyar British Council a Najeriya, Donna Mcgowan, ta tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da tallafa wa gwamnati wajen aiwatar da manufofin ilimi da haɓaka kwarewar malamai da tsarin koyarwa a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here