Gwamnatin Kano ta raba Babura domin ƙarfafa ayyukan masu bai wa dazuka kariya

xIMG 20260203 WA0024 1140x640.jpg.pagespeed.ic .Mfo7yvw4F 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙarfafa kare muhalli da sa ido kan gandun daji ta hanyar raba babura ga jami’an gandun daji da ke aiki a sahun gaba a yankuna shida na gandun daji a faɗin jihar.

Wannan shiri da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta aiwatar yana da nufin ƙara sauƙin motsi, hanzarta kai ɗauki, da tabbatar da ingantaccen sa ido kan wuraren ajiyar gandun daji.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Hashim, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin dakile ayyukan da ba su dace ba tare da bunƙasa kula da muhalli ta hanya mai ɗorewa.

An miƙa baburan a hukumance ga jami’an yankuna masu wakiltar Danbatta, Kano, Wudil, Gwarzo, Bichi da Tudun Wada ta hannun Sakataren Dindindin na Ma’aikatar, Mustapha Nuraddeen, a madadin kwamishinan.

Kwamishinan ya buƙaci jami’an su nuna ƙwarewa, jajircewa da gaskiya wajen kare albarkatun gandun dajin jihar, tare da jaddada cewa gwamnatin Abba Yusuf ta himmatu wajen samar da yanayin aiki mai kyau ga jami’an muhalli.

Daraktan Gandun daji, Malam Auwalu Muhammad, ya bayyana cewa tsawon fiye da shekaru ashirin jami’an gandun daji sun yi aiki da ƙarancin kayan tallafi, yana mai cewa raba baburan babban mataki ne da zai sauƙaƙa isa zuwa wuraren gandun daji masu nisa.

Yayin da wakilin masu cin gajiyar shirin, Murtala Sabo-Kachsko, ya tabbatar da cewa za a yi amfani da baburan yadda ya dace domin ƙara tsaurara kare gandun daji a jihar.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here