Gwamna Lawal ya amince da naɗin sabon Sarkin Gusau

IMG 20250729 WA0017

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau.

Alhaji Abdulkadir zai ɗare karagar ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar, inda zai maye gurbin mahaifinsa, Marigayi Mai martaba Dakta. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025.

Sakataren gwamnatin jihar ta Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar, inda ya ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa.

Sabon sarkin dai, shi ne babban ɗan marigayin, kuma kafin naɗa shi sarki, shi ne Bunun Gusau.

Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne.

Haka kuma yi kira ga sabon sarki ya dage wajen kira da samun haɗin kai da ci gaban masarautar Gusau da jihar, da ma ƙasar baki ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here