Guraben karatu na musamman: JAMB ta tantance ɗalibai 85 masu ƙananan shekaru don shiga manyan makarantu

Jamb

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) ta sanar da kammala tantance ɗalibai 85 mazu ƙananan shekaru waɗanda suka cancanci karɓa ta musamman a manyan makarantu bayan cikakken bincike.

A cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labaran hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ya fitar a ranar Litinin, JAMB ta bayyana cewa ɗaliban 85 ɗin sun cika sharuddan da aka shimfiɗa bayan gwaje-gwaje da matakai masu tsauri na tantancewa.

Hukumar ta ce dukkan ɗaliban da abin ya shafa ƙasa da shekaru 16 ne a watan Satumba 2025, amma an tabbatar da cancantarsu bayan bin matakai na musamman.

JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai 2,031,133 da suka rubuta jarabawar UTME ta shekarar 2025, ɗalibai 41,027 ne suka nemi shiga tsarin karɓa ta musamman, inda 599 suka samu kashi 80 cikin ɗari a jarabawar.

Hukumar ta ce waɗannan 599 sun sake fuskantar tantancewa ta takardun makaranta da jarabawar PUTME, inda 182 suka fito da sakamako mai kyau, daga ciki kuma 85 aka tabbatar da su don karɓar shiga manyan makarantu.

Haka kuma, hukumar ta umarci duk ɗalibai daga cikin 182 da suka rasa ganawar ƙarshe da hujja mai inganci, da su miƙa ƙorafi ta shafin JAMB Support Ticketing System a sashe mai taken “2025 Underage Complaint.”

JAMB ta ƙara da cewa waɗanda suka samu maki 320 da sama a UTME amma suka kasa ɗora sakamakon O’Level za su iya yin hakan cikin kwanaki biyu kafin ranar Laraba, 29 ga Oktoba, 2025.

Hukumar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da kare gaskiya, adalci da sahihancin ilimi a dukkanin matakai na karatun manyan makarantu a ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here