Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da firaministan Birtaniya Keir Starmer a ranar Asabar, inda ya bayyana damuwa kan yadda rikicin da ya biyo bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran ke ƙara kamari.
Erdogan ya ce Turkiyya na sa ido sosai kan halin da ake ciki tun bayan fara hare-haren kan Iran.
Ya bayyana cewa idan aka ci gaba da irin waɗannan tsoma bakin na tsawon lokaci, za su iya jawo babbar barazana ga zaman lafiyar yankuna da kuma na duniya baki ɗaya.
Ya kuma nuna cewa har yanzu akwai matakan da za a iya ɗauka domin samar da dandalin tattaunawa, yana mai cewa ƙoƙarin samar da zaman lafiya na ƙasarsa na ci gaba.
Shugaban na Turkiyya ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar waya da Starmer, kamar yadda wata sanarwa ta hukuma daga daraktan sadarwa na ƙasar Turkiyya ta tabbatar.
Tattaunawar ta kuma shafi dangantakar ƙasashen biyu da kuma wasu muhimman batutuwan yankuna da na duniya.
Sanarwar ta ce Erdogan ya sake jaddada ƙudirin Turkiyya na ƙarfafa haɗin gwiwa da Birtaniya a fannoni daban-daban, musamman a masana’antar tsaro.
Ya kuma ƙara da cewa ƙasarsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da za su bunƙasa wannan haɗin gwiwa.













































