CISLAC ta soki Wike kan cin zarafin Soja, yayin da Najeriya ke fuskantar barazanar ƙasashen waje

WhatsApp Image 2025 11 11 at 2.25.36 PM 1 750x430 (1)

Ƙungiyar sa ke sanya idanun kan ayyukan majalisun dokokin kasar nan da yaki da cin hanci da rashawa (CISLAC) ta bukaci jami’an gwamnati su rika nuna ladabi da kamun kai wajen aiwatar da ayyukansu, tana gargadin cewa rashin ladabi da hali na raini daga jami’an gwamnati na iya gurbata sunan tsarin mulkin Najeriya a idon kasashen duniya.

A cikin wata sanarwa da shugaban CISLAC kuma shugaban Transparency International reshen Najeriya, Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani) ya sa hannu, cibiyar ta bayyana cewa jami’an gwamnati suna da alhakin kasancewa masu ladabi, kamun kai da kuma bin ka’idojin gudanar da aiki a ofisoshin gwamnati.

CISLAC ta nuna damuwa kan abin da ta kira rashin ladabi da rashin mutuntawa da ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike ya yi, yayin wata cacar baka tsakaninsa da jami’in soji, tana mai cewa irin wannan hali bai dace da wanda ke rike da mukamin gwamnati ba, kuma yana nuna raini da girman kai da bai kamata a nuna ba.

Sanarwar ta kara da cewa halin da Wike ya nuna tun daga lokacin yana gwamna har zuwa yanzu na nuna rashin nutsuwa da rashin iya sarrafa fushi, wanda ke nuna karancin ƙwarewa da mutunta iyakokin tsarin mulki da dokoki.

CISLAC ta tuna cewa kwanan nan wasu kungiyoyin fararen hula sama da 52 masu aiki kan yaki da cin hanci da rashawa da inganta gaskiya da rikon amana suka bukaci a gudanar da bincike kai tsaye kan Wike saboda zargin boye kadarori da samun dukiya ta hanyar da ba ta dace ba da kuma karya dokokin bayyana kadarorii.

Labari mai alaƙa: Cin zarafin da Wike ya yiwa soja a bainar jama’a, babbar barazana ce ga tsaron ƙasa – Buratai

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa CISLAC ta bayyana cin mutuncin da Wike ya yi wa jami’in soja a bainar jama’a a matsayin abin kunya da rashin mutunci ga tsaron kasa, musamman a wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro da kuma matsin lamba daga kasashen duniya.

CISLAC ta yaba da natsuwar jami’in sojin da ya nuna kwarewa da kamun kai duk da yadda aka tsokane shi, tana mai cewa hakan na nuna nagartar horo da mutuncin rundunar sojin Najeriya.

Rafsanjani ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauki mataki mai tsauri, yana mai cewa bai kamata wadanda ke da hali na rashin kamun kai da raina dokoki su ci gaba da rike mukamai ba.

CISLAC ta kuma bukaci Wike ya nemi afuwa daga jami’in da abin ya shafa, rundunar sojin Najeriya da kuma shugaban kasa, tana mai cewa ya zama wajibi a dinga fifita kare martabar kasa da tsaron kasa a kowane lokaci.

Ta kammala da cewa lokaci ya yi da shugabanci zai rika karfafa amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati, ba ya raunana su ba, domin martabar rundunar soji da kuma kyakkyawan sunan Najeriya a idon duniya na bukatar hakan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here