Bayern Munich ta doke PSG mai rike da kofin gasar zakarun Turai da ci 2-1 a birnin Paris

AFP 20251104 832P6ZE v3 MidRes TopshotFblEurC1PsgBayern 750x430

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta ci gaba da jan ragamar wasanninta bayan ta doke Paris Saint-Germain mai rike da kofin gasar zakarun Turai da ci 2-1 a filin Parc des Princes da ke birnin Paris a ranar Talata.

Luis Diaz ya fara zura kwallo ta farko a minti na huɗu sannan ya sake cin ta biyu bayan mintuna 30, duk a cikin rabin lokaci na farko.

Sai dai daga baya aka kore shi daga wasa bayan ya yi wa Achraf Hakimi na PSG rauni sakamakon bugun da ya yi masa, wanda ya sa ɗan wasan na Morocco ya bar fili cikin hawaye.

Joao Neves ne ya ci kwallo ɗaya tilo da ta rage tazarar PSG a minti na 74, amma hakan bai hana Bayern kare nasararta ba duk da cewa ta buga rabin lokaci na biyu tana da mutum ɗaya kaɗai bayan korar Diaz.

Nasarar ta tabbatar da cikakkiyar bajintar Bayern wadda ta ci duk wasanninta 16 na bana, ciki har da wasanni hudu na gasar zakarun Turai, inda ta zura kwallaye 56 gaba ɗaya tare da samun maki 12 kamar Arsenal.

A gefe guda, PSG ta gamu da ƙarin matsalar rauni bayan dan wasan Ousmane Dembele ya sake jinyata, lamarin da ya ƙara dagula tsarin ƙungiyar a wannan kaka.

Rashin lafiyar Achraf Hakimi wanda ake sa ran zai jagoranci tawagar Morocco a gasar cin kofin Afrika mai zuwa, na iya zama babban kalubale ga PSG, duk da cewa har yanzu suna da damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Haka kuma, wannan wasa ya zama maimaituwar wasan karshe na shekarar 2020 da Bayern ta yi nasara da ci 1-0, abin da ya kara tabbatar da karfinta a gasar zakarun Turai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here