CAF: Chiamaka Nnadozie ta sake lashe kyautar mai tsaron raga mafi kyau a Afrika karo na uku a jere

chiamaka nnadozie 1

Mai tsaron raga a ƙungiyar ƙwallon ƙafar Mata ta Najeriya Chiamaka Nnadozie ta lashe kyautar mai tsaron raga  mafi kyau a Africa karo na uku a jere wanda hukumar kwallon kafar Afrika CAF ke shiryawa duk shekara.

Nnadozie ta samu kyautar ne a ranar Laraba a birnin Rabat na ƙasar Morocco yayin bikin bayar da kyaututtuka na CAF na shekarar 2025.

Nnadozie ta zarce Khadija Er-Rmichi ta Morocco da Andile Dlamini ta Afirka ta Kudu wajen samun wannan girmamawa, lamarin da ya ci gaba da tabbatar da matsayinta a matsayin jagorar masu tsaron raga a nahiyar Afrika.

A shekarar 2025, Nnadozie ta yi fice a kungiyarta ta Paris FC inda ta taimaka wajen lashe gasar Coupe de France Féminine, sannan a matakin kasa ta taka muhimmiyar rawa wajen lashe gasar cin kofin mata ta Afrika karo na goma, inda ta kare raga sau hudu tare da karɓar kyautar ƙwararriyar mai tsaron raga ta gasar.

Bayan gasar cin kofin Afrika, ta koma kungiyar Brighton Hove Albion ta kasar Ingila inda ta fara da nasara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here