Ƴan sanda sun gano motar da aka sace ta tawagar mataimakin gwamnan Kano, sun kama wanda ake zargi

Kano State Govt. House 1

Ofishin mataimakin gwamnan jihar Kano ya tabbatar da cewa motar Toyota Hilux da aka sace kwanan nan daga jerin motocin mataimakin gwamnan an sake ganinta bayan aikin haɗin gwiwa na jami’an tsaro.

Bisa ga rahoton da aka samu daga rundunar ‘yan sanda, an gano motar ne da safiyar Laraba bayan wani binciken gaggawar da jami’an tsaro suka gudanar cikin kwarewa.

Binciken ya gano cewa wani direba da ke da cikakken matsayin ma’aikaci na dindindin a ofishin gwamnatin jihar an kama shi bisa zargin satar motar, kuma yanzu haka yana taimakawa jami’an tsaro wajen ci gaba da bincike.

Ofishin mataimakin gwamnan ya yaba da gaggawar martani da kwarewar da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka nuna wajen gano motar da akaa gano.

Karin labari: Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin ya saci mota a fadar gwamnatin Kano

A cikin sanarwar da sakataren yada labaran mataimakin Gwamnan Ibrahim Garba Sgu’aibu ya fitar ranar Laraba, ya bayyana cewa abin da ya faru ya nuna cin amana da rashin gaskiya daga wanda aka kama.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa jama’a su kwantar da hankalinsu domin gwamnati na ci gaba da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a ciki da wajen gidan gwamnati na jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here