Wata tawagar ’yan jarida su 13 daga kafofin watsa labarai daban-daban sun hadu da hatsarin mota yayin da suke aikin rufe bikin ƙaddamar da ayyuka da Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa Maso Gabas NEDC ke gudanarwa a jihar Bauchi.
Hatsarin ya faru ne a yayin rangadin duba ayyuka a fadin jihar a ranar Juma’a, wanda Ministan ƙasa mai kula da bunƙasa yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu, ya jagoranta.
Hatsarin ya auku ne a kan titin Yashi zuwa Yelwan Duguri da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi, jim kaɗan bayan tawagar ta kammala ƙaddamar da aikin makarantar sakandaren gwamnati a Yelwan Duguri.
’Yan jaridan sun samu raunuka mabambanta, inda aka garzaya da su asibitin Yelwan Duguri domin samun agajin gaggawa, kafin daga bisani a shirya mayar da su asibitin koyarwa na ATBU domin ƙarin kulawar lafiya.
Daga cikin ’yan jaridan da suka jikkata akwai wakilin kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, wakilai daga jaridun The Guardian da The Nation, da wakilin gidan talabijin na ƙasa NTA tare da mai ɗaukar hotonsa, wakilai da masu ɗaukar hoto daga Channels Television da Arise TV, wakilin AIT, ’yan rahoto biyu daga Bauchi Radio Corporation BRC, mai ɗaukar hoto daga gidan Radiyon jihar Bauchi BATV, wakilin kafar labarai ta internet, da direban motar.
Mambobin tawagar sun haɗa da Ministan ƙasa mai kula da bunƙasa yankuna, shugaban hukumar da babban daraktanta, mataimakin gwamnan jihar Bauchi, da sauran jami’an gwamnati.













































