Kungiyar marubuta wasanni ta ƙasa (SWAN) ta kaddamar da asusun tallafi na naira biliyan biyu domin gina hedkwatarta a birnin tarayya Abuja.
Shugaban ƙasa na SWAN, Isaiah Benjamin, ne ya bayyana kaddamarwar yayin bikin cika shekara sittin da kafuwar ƙungiyar a ranar Juma’a a Abuja.
Benjamin ya yaba wa mambobin SWAN bisa jajircewarsu da gudunmawarsu tun daga kafuwar ƙungiyar, inda ya ce shekaru sittin na nuni da girma kuma lokaci ne da ya dace ƙungiyar ta samu wurin zama nata na dindindin.
Ya kuma bayyana cewa bikin cika shekara sittin ba kawai na nuna tsawon lokaci bane, amma dama ce ta sake tabbatar da manufa da jajircewar ƙungiyar wajen ci gaba da tallafa wa ci gaban labaran wasanni a ƙasar.
Ya ƙara da cewa aikin labaran wasanni ba wai kawai bayar da rahoto kan sakamakon wasa ba ne, illa dai shimfiɗa gada tsakanin ‘yan wasa da magoya baya, da kuma tsakanin manufofi da aiwatarwa a harkokin wasanni.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayar da rahoton cewa SWAN an kafa ta ne a shekarar 1964, inda ta cika shekara sittin a 2024, amma aka dage bikin zagayowar zuwa 2025.
NAN











































