Zambar Naira Biliyan 10: Magatakardar kotu ya amince da yin nagudu a shaidun shari’ar Ali Bello, alkali ya bayar da umarnin bincike

Ali Bello the Chief of Staff to Kogi governor Usman Ododo

Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba wa rundunar ƴan sandan Nijeriya da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta DSS umarnin gudanar da bincike kan wani magatakardar kotu mai suna Nasiru Zubairu da kuma wanda ake tuhuma na biyu, Daudu Sulaiman, bisa zargin yin magudi da shaidu a shari’ar damfara ta Naira Biliyan 10 da ke gudana ta Ali Bello.

Wannan umarni ya biyo bayan bayani da alkalin kotu, James Omotosho, ya bayyana cewa magatakardar kotun ya shaida masa cewa Daudu Sulaiman ya tuntube shi domin ya goge wasu saƙonnin WhatsApp daga wayar salula da aka karɓa a matsayin shaidu masu lamba N da O a shari’ar.

A hukuncinsa na ranar Alhamis, alkalin kotun ya kunna abin da ya bayyana a matsayin furucin magatakardar kotun a bainar jama’a, sannan ya umurci Nasiru Zubairu da ya ba da cikakken bayani a gaban kowa kan abin da ya faru tsakaninsa da wanda ake tuhuma.

A cewar sanarwar da kakakin Hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, alkalin kotun ya bayyana cewa akwai manufar bayyanawa da fallasa gaskiya a Kotun Tarayya, tare da jaddada cewa babu sassauci ko yafiya ga irin wannan hali, sannan ya ce wanda ake zargi yana nan a kotu domin a ji bayaninsa kai tsaye.

Daudu Sulaiman shi ne wanda ake tuhuma na biyu a shari’ar wankiyar kuɗi ta Naira Biliyan 10, inda ake tuhumarsa tare da Ali Bello, ɗan uwan tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.

Ana zargin su da karkatar da kuɗaɗen gwamnatin Jihar Kogi har Naira Biliyan 10 a lokacin da Yahaya Bello yake gwamna, yayin da shi kansa Yahaya Bello ke fuskantar tuhuma a gaban kotuna biyu bisa zargin damfara da ta shafi wa’adinsa na shekaru takwas a matsayin gwamna.

A yayin zaman kotu na ranar Alhamis, Nasiru Zubairu ya amsa cewa wanda ake tuhuma na biyu ya nemi sanin abin da yake buƙata, inda ya bayyana masa cewa yana da matsalar masauki.

Ya ce an nemi ya goge wasu bayanai da saƙonnin WhatsApp daga shaidun da ke gaban kotu, tare da masa alƙawarin ba shi gida idan ya aiwatar da hakan.

Alkalin kotun Omotosho ya amince da buƙatar Daraktan Gurfanarwa na Ƙasa, Rotimi Oyedepo, Babban Lauya mai matsayi na SAN, domin ya jagoranci jami’in binciken gwamnati na EFCC, Muhammed Abubakar, ya tabbatar ko da gaske an goge saƙonnin daga wayar.

Muhammed Abubakar ya shaida wa kotu cewa an goge saƙonni da dama daga shaidu N da O, waɗanda suka shafi shekarun 2020 zuwa 2022, inda ya ce akwai gibin saƙonni daga 22 zuwa 29 ga Disamba 2020, tare da bacewar wasu saƙonni masu muhimmanci da ke ɗauke da bayanan jigilar kuɗaɗe da suka haɗa da miliyoyin Naira a lokuta daban-daban.

Ya ƙara da cewa wasu saƙonni na watan Janairu da Agusta 2021 da Fabrairu 2022 da ke nuni da karɓa da jigilar kuɗaɗe sun ɓace gaba ɗaya, duk da cewa ya taɓa ganinsu a lokacin binciken da ya gudanar tun farko.

Biyo bayan wannan, Rotimi Oyedepo ya roƙi kotu da ta bayar da umarnin gudanar da binciken kan shaidar N tare da soke belin wanda ake tuhuma na biyu, yana mai cewa akwai babban zargi da shakku mai ƙarfi na cewa an yi magudi da muhimmiyar shaida.

Lauyan wanda ake tuhuma ya bayyana mamakinsa kan lamarin, amma ya roƙi kotu da ta jira sakamakon binciken kafin ɗaukar wani mataki na gaba.

Alkalin kotun ya umurci rundunar ƴan sanda da DSS da su gudanar da bincike kan zargin, sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa 9 ga Fabrairu domin ci gaba da shari’a.

Shari’ar ta fara ne tun shekarar 2022 bayan Hukumar EFCC ta shigar da ƙara kan Ali Bello da Daudu Sulaiman, tana zarginsu da aikata laifukan damfara da wankiyar kuɗi da suka shafi kuɗaɗen gwamnatin Jihar Kogi, tare da ambaton wasu mutane da suka haɗa da Abdulsalami Hudu da tsohon gwamna Yahaya Bello,

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here