Laftanar A.M. Yarima daga rundunar sojin ruwa ta Najeriya ya tsira daga wani yunƙurin hallakawa da aka yi masa a dare Lahadi bayan takaddamar da ta faru tsakaninsa da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike.
Rahotanni daga rundunar soji sun bayyana cewa wasu mutane da ba a gane su ba sanye da kaya baƙaƙe suna cikin motoci biyu nau’in Hilux marasa lambar rijista suka fara binsa tun daga tashar mai ta NIPCO da ke kusa da Line Expressway zuwa Gado Nasco.
Rahoton ya ce, motocin sun ci gaba da binsa kai tsaye zuwa Gado Nasco Way ba tare da katsewa ba, abin da ya tabbatar masa cewa ana bibiyar motsinsa a ɓoye.
Laftanar Yarima ya lura da wannan yanayi, sannan ya yi amfani da dabara ta canza hanya da nufin kawar da waɗanda ke binsa.
Dabarar da ya yi ta ba shi damar kubuta daga cikin haɗarin, inda ya samu ya nisanta kansa daga motocin da ake zargi.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne kusan ƙarfe shida da rabi na yamma, abin da ya sa ake tantama kan musabbabin wannan yunƙurin kisa ne.













































