Shugaban tashar Hikima Radio ya ajiye aiki

IMG 20260205 WA0008 2 750x430

Malam Abubakar Isah Dandago ya sauka daga mukaminsa na shugaban tashar Hikima Radio, inda ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa tsarin da aka shimfiɗa da kuma yardar Allah.

Ya sanar da ajiye aikin ne ta cikin wata sanarwa ta kansa da ya raba a ranar Alhamis, inda ya sanar da shugabanci da ma’aikatan gidan rediyon game da ficewarsa daga mukamin.

Ya bayyana cewa ya ajiye aikin kamar yadda aka nema, tare da bayyana fatan cewa wannan mataki zai zama alheri ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, yana mai jaddada cewa duk da bin ka’idoji da tsari, lamarin ya zo ne bisa ƙaddara.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa murabus ɗin wannan gogaggen ɗan jarida daga gidan rediyon ba ya rasa nasaba da sabani da ya shiga tsakaninsa da kwamitin daraktocin gidan rediyon.

Tsohon babban daraktan ya nuna matuƙar godiya ga mai gidan rediyon da shugabancinsa bisa amincewar da suka ba shi a lokacin da yake kan kujerar, yana mai cewa a ƙarƙashin jagorancinsa Hikima Radio ta samu gagarumin ci gaba fiye da yadda aka zata tun farko, wanda ya danganta da haɗin kai da taimakon Allah.

Ya kuma bayyana cewa ya bar ofis ba tare da wata ƙiyayya ba, yana mai neman afuwa daga duk wanda ya taɓa samun rashin jituwa da shi a lokacin aikinsa, tare da bayyana yafiya ga kowa, yana roƙon Allah ya kawo gafara da sulhu a tsakanin kowa da kowa.

Malam Abubakar Isah Dandago ya jaddada cewa alaƙarsa da Hikima Radio za ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi duk da murabus ɗinsa, yana mai cewa zai ci gaba da tallafa wa gidan rediyon da cigabansa a nan gaba, tare da yi wa magajinsa fatan alheri da nasara a aikinsa, yana kuma addu’ar samun kariya da ɗorewar ci gaba ga gidan rediyon da ma’aikatansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here